GABATARWA:
TSANANI, TSANGWAMA DA HADARIN DA HAUSAWA MABIYAN ALMASIHU KE FUSKANTA
Hakika tsanani da tsangwama, da hadarin da mabiyan Almasihu, wato Hausawa Kristoci ke fuskanta a Nigeria yakai intaha.
GA WASU KALILAN DAGA CIKIN TSANANIN DA HAUSAWA MABIYAN ALMASIHU KE FUSKANTA A NIJERIYA:
- Hanamu sanuwa a duniya da gangan ta hanyoyin mana shamaki a kowanne fanni a Nigeria ta Arewa; ana nunawa duniya cewar ba bu wani bahaushe ko bahaushiya maibin Almasihu, sai dai yan tsararu dake cigaba da riko da addininsu na gargajiya wato maguzanci. Suna ta kirarin babu bahaushen daba masallacibane. Wannan kirarin yasa ake ci gaba da gallazawa mutanenmu azaba ta ko wace fuska.
- Hanawa yaranmu izinin shiga makarantu ,kin basu takardun shaidar yan kasa, kin daukan su ayyuka a fannonin ko ma’aikatun gwamnati massamman dai wadanda ke da sunayen Kristanci ko nasara!
- Yin amfani da kowace irin dama wajen ta da hankalinmu da haddasa yamitsin da ke kaiwa ga gone mana Majami’un mu da gidajen mu na kwana da kwashe mana mallakokinmu, yiwa wasu matayenmu fyade da cin zarafi da sauran nau’oin cin zarafin biladama.
- Kone mana wuraren ibadumu, da hana mu izinin gina wurin sujadunmu da aka kone mana a gwamnatance
- Dauke mana yaya da tilasta masu shiga musulinci ta ko wane hali. Tsorata su, suyi musun iyayen su da yi masu aure irin na kama-karya ba tare da sanin ko izinin iyayensu na haihuwa ba
- Hana mana abubuwan more rayuwa kamarsu hanyoyi, wutar lantarki, da ruwa da asibitoci da ko wane irin dausayi da ake samu a siyasance daga gwamnatocinmu.
- Hanawa mutanenmu dammar su fito a dama dasu a fagen siyasa ta wurin hana mana akwatin zabe, kin bamu masarautu da mukaman siyasa a Arewa kwata, dukda muna muna da mutane da suka can-canta ayi dasu ta fuskar ilimi da kuma kowacce irin kwarewa ta rayuwa. Amma sai aka yi mana shamaki da musulunci.
- Wata gawartacciyar matsala itace ta kwachewa mutanenmu gonakinsu na gado dama wasu gidaje da muka gada kaka da kakanni. Wannan aika aika na faruwane da sanin sarakunan nan na musulunci da aka dora mana karfi da yaji.
- Mabiyan Almasihu dake arewacin Nigeria na cikin mummunan kunci na rayuwa sanadiyar kisa da iya cin hatsi na musulunci da niyyar musuluntar da arewa ta ko wane hali. Abin takaicin shine ana gudanar da wannan mugun aikin da baitunmalin kasa, wato gwamnati ta wurin bunkasa ayyukan ta’adda da firgitar da rayuwar yan kasa. Arewarmu ta Nijeriya ayau ta zama saduma da gwamratar karshen zamani inda gaskiya da amana suka kaurace, tashin hankali da keta ya sami gindin zama. fadin gaskiya da aikata ta ya zama babban kalubalen da sai wadanda suka sai da ransu kawai ke kamantashi.
- Tsaron dukiya da na rayuwarmu ya tabarbare. Hakika tsananin da muke sha a Kristance yafi gaban rashin kayayyakin more rayuwa irinsu hanya, ruwansha, asibutoci ko makarantu. Abin yakai ga ana ta farautar rayukan mu da yan abubuwan da muke samu da jibin goshi. Anatayi mana fashi da makamai, ana ta garkuwa da mutanenmu da karbar makudan kudaden fansa. Mun zama maraya duk da muna gaban iyayenmu. Allah kadai ya sauro wajen taimakon mu!
BABBAN UMURNIN CIBIYAR HAUSAWA KRISTA TA NIGERIA (HAUSA CHRISTIANS FOUNDATION – HACFO)
KUDIRINMU
JIGON WANZUWARMU
MANUFARMU
Nunawa ko koma sanar da daukanci duniya cewa akwaimu anan Arewacin Nijeriya kuma mu yan kasane, Nigeria tamuce muma, muna kuma tinkaho da kasancewarmu na Almasihu a Kristance. Karfafawa da kuma goyon bayan dukan Kristoci Hausawa da su fito fili su bayyana zaluncin da suke fuskanta a duk inda suke a zaune; da kuma ci gaba da jajircewar neman yancin aikata bangaskiyarmu ta Krista batare da tsangwamaba kamar dai yadda sauran yan kasa ke nasu badali mu ma a sakar man mara! Ta haka zamu kare, mu kuma gina Hausawa Krista, mu kuma ribato sauran da har yanzu basu san Almasihu ba.
AYYUKANMU
- Kai Bishara
- Bunkasa Ilimi da Inganta Rayuwa
- Aikin Kiwon Lafiya da Bukatun Dan’adam
- Watsa Labaru
- Kare Hakin Bil’adama (Kristocin Arewacin Nijeriya)
A KARSHE
KALMAR TUSHEN KAMANIN HAUSAWA KRISTA
Ana wahalshe mu ta kowacce hanya, duk da haka, ba a ci dunguminmu ba. Ana ruda mu, duk da haka bamu karai ba. Ana tsananta mana, duk da haka bamu zama yasassu ba. Ana fyada mu a kasa, duk da haka ba a hallaka mu ba. Kullum muna a cikin hatsarin kisa, irin kisan da aka yi wa Yesu, domin a bayyana rayuwar Yesu ta gare mu. Wato muddin muna raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, domin a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa. Ta haka mutuwa take aikatawa a cikinmu.
Tun da yake muna da ruhun bangaskiya iri daya da na wanda ya rubuta wannan, “Na gasgata, saboda haka na yi magana,” to, mu ma mun gasgata, saboda haka muke magana. Mun sani shi wannan da ya ta da Ubangiji Yesu daga matattu, mu ma zai tashe mu albarkacin Yesu, ya kuma kawo mu a gabansa tare da dukan Masubi.
Amin!
BUKATAR BISHARA
GABATARWA
- Me ke kara kyau a cikin duniya?
- Yake-yake da jita-jitan yaki ta ko ina.
- Jini ya zama abin gani yau da kullum fiye da ruwa a wurare daban-daban
- Rayukan jama’a ba a bakin komai suke ba.
- Begen mutane sai kara sanyi yake a duk wucewar sa”a
- Rayuwa na kara zama sai wani da wani
- Tashin hankali da yamutsin karshen zamani sai karuwa suke yi
- Ana karkashe Krista, kona Cocika, an hana abubuwan more rayuwa, sa rai duk ya dusashe
ME YA KAWO HAKA?
- Dalilin wadannan shine gaba da mulkin duhu yake da mulkin Ubangiji.
- Magabci yasan yana da karancin lokaci, ya fito da karfi don ya sace, ya kashe dakuma hallakar.. Balrazanar da ake a duniya, don hana Ikilisiya cika kudirin ta ne: Babban Umurni
- Idan tsoro ya hana Ikilisiyar cika babban umurnin, sai Shaidan ya sami karfin dakile ayukan mutane a duniya.
- Kuma masifu ba zai taba yankewa ba, muddin shaidan na jan gaba
- Duniya na bukatar Kristi amma shaidan na kokarin hana Ikilisiya isar da sakon bishara.
INA MAFITA?
- Maganin wadannan masifu ba zai taba samuwa ba a cikin duniyar nan, sai cikin Yesu kadai
- Salama na samuwa cikin Almasihu kadai, Yesu a shirye ya ke domin ya ceci Ikilisiya amma sai mun yi biyayya mun kuma cika umurnin
- Kowanne Krista dole ya tashi tsaye don tabbatar da nasarar Almasihu akan shaidan ta wajen jajircewa cikar babban umurni ga dukan kasashe, ta haka za a hanzarta dawowar Yesu Almasihu
GASKIYAR MAGANA
- Kafin dawowar Yesu, dangon zuwan Almasihu yawaitan tsanani.
- Hanzarta dawowar Almasihu ya ta’alaka a kan kowanne mai bi wajen yin wa’azin bishara ga kowace kabila.
- Kowanne Krista dole ya tashi tsaye don tabbatar da nasarar Almasihu akan shaidan ta wajen jajircewa cikar babban umurni ga dukan kasashe, ta haka za a hanzarta dawowar Yesu Almasihu
- Akwai mutane da yawa a raye da ba su san Yesu ba, fiye da kowanne lokaci cikin tarihi
- Wannan na nuna cewa babban aikin bishara bai kare ba!
- Yin bishara yadda aka saba ba zai sa agama aikin ba
- Bishara dole ta zama jigo kowacce Ikilisiya
- Dole Ikilisiya ta zuba jari cikin aikin bishara yadda yakamata
- Dawowarsa da wuri, alheri ne ga Ikilisiya
KIDIDDIGA A DUNIYANCE (ABINDA BINCIKE YA NUNA A DUNIYA)
- Kashi 81 cikin 100 na, Hindawa, Musulmai da Budawa basu san mutum daya mabiyin Yesu Almasihu ba
- Akwai al’umai daban daban 16,560 a duniya a yau
- Mutane 47,000 na mutuwa a kullum wadanda bishara ba ta kai gare su ba, ba tare da sun hadu da mabiyin Yesu Almasihu ba.
- Akwai kimanin mutane Biliyan 7.13 mutane a duk duniya
- Kimanin Biliyan 4.8 ne ba Krista ba (67%)
- Kimanin Biliyan 2.91 ne wadanda ba a kai wa bishara ba.
- A kimance, 40.5% na al’umai basu riga sunji bishar ba
- Katuna 47,000 na mutuwa a kullum wadanda bishara ba ta kai gare su ba, ba tare da sun hadu da mabiyin Yesu Almasihu ba.
- Ya za kaji a ce ka gama dukar rayuwarka ba tare da sanin Kristi ba?
- Aiyana abun a ranka, “da ace kai ne
TARUN JAMA’A HAUSAWA
- Akwai addini uku cikin al’uman Hausawa a Najeriya: Krista, Musulunci da Maguzanci
- Fiye da miliyan 20 na Hausawa a Najeriya da ba su sami jin labarin bisharar yesu Almasihu ba. Kusan 60% na mutanen ba su taba haduwa da kowanne irin mai bisharar Almasihu ba
- Kasar Hausa a nune take domin babban girbi na rayuka amma darurruka na mutuwa da hallaka a kulliyomin, saboda kadan daga cikin Krista ne suke shirye su kai bisharar kaunar Yesu.
- Yawancin mutane a kasar Hausa na so su zo ga Yesu amma tsoron rasa ransu na hana su, kuma Kristoci kalilan ke shirye su yadda su karbe su in sun karbi Yesu Almasihu
- Tsananin kiyayya da kristoci ke fuskanta a Arewacin Najeriya, masamman Hausawa kristoci, na karuwa a kowace rana. Wuya da kunci sun zama ruwan dare, kuma rayuwa na cikin halin hawula’i
- Kristoci na rasa rayukan su da dukiyoyinsu a kowace rana. Sababbin tuba na fuskantar rasa rayukan su, ko matsanaciyar wahala dun suyi musun Yesu Kristi
- Kasar Hausa ta zama wuri mai wuya ga duk wani ayuka na Kristanci.
MAI YUWUWA NE
- Da Yesu ya aike mu isar da bishara ga al’umai 6,698, ya bamu TANAJI don AIKIN
- Cikin kowarce albarka akwai kwayar bishara
- A duk lokacin da aka albarkace mu, an kudirta mana mu zama masu albarka
- Ba nufin Allah bane, ko daya daga cikin hausawa su hallaka, amma kowa yazo ga tuba (2 Bitrus 3:9)
- Rayuwar mu a duniyar nan ta kankanen lokaci ce. Ba ma bukatar tsaro mai shudewa. Daukaka Ubangiji shi ne manufar mu. A karshen rayuwa za mu so muji, “Madalla bawan kirki,, mai aminci. Ka yi gaskiya a kan karamin abu, zan dora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da Ubangidanka”(Matiyu 25:21)